Kungiyar likitocin farfadowa ta kasar Sin kungiya ce ta ilimi ta kasa da aka kafa a shekarar 1983 tare da amincewar ma'aikatar kiwon lafiya, kuma ta yi rajista a ma'aikatar kula da fararen hula. Ta shiga kungiyar kimiya da fasaha ta kasar Sin a shekarar 1987, da kungiyar likitoci ta kasa da kasa a shekarar 2001, da kungiyar likitocin kiwon lafiya ta kasa da kasa a shekarar 2001. Cibiyar tana cikin asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Japan dake nan birnin Beijing.